in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan zai halarci taro game da wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu
2017-06-12 09:40:18 cri

Wata sanarwa da sakataren ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan Abul-Ghani Al-Naeem ya fitar, ta ce shugaban kasar Omar Al-Bashir zai halarci wani taron shugabanni, domin tattauna yanayin da ake ciki a Sudan ta Kudu, da ma matakan da ake dauka na wanzar da zaman lafiya a kasar.

Taron wanda kungiyar bunkasa ci gaban kasashen gabashin Afirka ta IGAD za ta shirya a birnin Addis Ababan kasar Habasha a Litinin din nan, zai kuma dubi irin matakan da ake dauka game da tabbatar da tsaro a Sudan ta Kudun, da ma kalubalen da ake fuskanta wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar kasar ta watan Agustan shekarar 2015.

Abul-Ghani Al-Naeem ya ce, shugaban na Sudan ya amince ya halarci taron na wannan karo ne, sakamakon sha'awar da yake da ita ta ganin an gaggauta warware rikicin dake addabar Sudan ta Kudu.

Sanarwar ta kara da cewa, a 'yan kwanakin baya, Mr. Al-Naeem ya gana da jami'in diflomasiyyar Amurka dake birnin Khartoum Steven Koutsis, game da yunkurin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudun, a wani mataki na share fagen taron da kungiyar ta IGAD za ta gudanar. Kuma sassan biyu sun amince da batun tsagaita wuta, a matsayin muhimmin mataki da ya wajaba a dauka a kasar, da ma yunkurin da IGAD ke yi na wanzar da zaman lafiya da lumana a jaririyar kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China