in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yabawa jami'an UNMISS wajen kai dauki game da halin da ake ciki a kasar
2017-06-22 11:11:20 cri

Babban jami'in MDD a Sudan ta kudu ya yaba bisa namijin kokarin da tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD ke gudanarwa wajen tallafawa shirin kai dauki don tallafa wajen shawo kan matsanancin halin da al'umma ke ciki a sanadiyyar tashe tashen hankula a kasar.

Shugaban tawagar MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta kudu (UNMISS) David Shearer, ya bayyana cewa, wannan namijin kokarin da jami'an tawagar wanzar da zaman lafiyar ke aiwatarwa zai iya shawo kan tabarbarewar al'amurra a kasar Sudan ta kudun.

Shearer, yana jawabi ne a Aburoc dake yankin Upper Nilu inda akwai mutane kimanin 25,000 dake neman mafaka a sanadiyyar tashin hankali, ya ce, zuwan tawagar wanzan da zaman lafiyar yankin ya kara tabbatar da tsaron lafiyar jami'an aikin ba da agajin gaggawa.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a Juba bayan ziyarar da ya kai, Shearer ya bayyana cewa, zaman jami'an wanzar da zaman lafiya a yankin ya taimaka wajen samar da tsaro da kuma kwarin gwiwa ga hukumomin ba da agajin wadanda suke son gudanar da ayyukansu a yankuna masu fama da hadari.

Kauyen wanda ke da yawan jama'a kimanin 5,000 kafin zuwan masu neman mafakar, a yanzu yana fama da karancin abinci da ruwan sha da karancin cibiyoyin kula da lafiya.

A cewar jami'an MDD, saboda wannan damar da aka samu, Aburoc zai iya zama yankin na musamman na samar da ayyukan jin kai ga masu fama da bala'in, kasancewa jama'a suna taruruwar zuwa yankin cikin gaggawa.

Ya ce, yana matukar farin cikin sakamakon yadda jami'an wanzar da zaman lafiyar ke ci gaba da tura jami'ai da ke aiki matuka a yankin.

Tawagar wanzar da zaman lafiya na MDD ta tura jami'ai 80 daga Ruwanda tare da motoci dauke da kayan yaki zuwa Aburoc a farkon watan Aprilu, inda suka samar da ingantuwar yanayin tsaro kwanaki biyu gabanin isar masu bayar da tallafin jin kai ga al'ummar yankin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China