A wata sanarwar da SACH ta fitar a jiya Jumma'a, ta bayyana cewa "muna yin Allah wadai kuma mun kalubalanci matakin sayar da kayayyakin tarihin gargajiya na kasarmu ba bisa ka'ida ba. Muna fatan kungiyoyi da daidaikun al'umma za su mutunta yarjejeniyar kasa da kasa, kuma su mutunta martabar al'umma da al'adunsu na gargajiya, kuma a yi kaffa-kaffa wajen sayar da kayayyakin gargajiya na wata kasa ta barauniyar hanya".
A kwanan nan ne hukumar ta SACH, ta fitar da wasu dokoki da suka haramta yin gwanjon kayayyakin tarihi na kasar Sin wadanda aka fice da su daga kasar ta haramtattun hanyoyi.
A wata sanarwar da ta gabatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, SACH, ta ce ta yi nasarar dakile aniyar Japanawa a yunkurinsu na yin gwanjon kayayyakin tarihin gargajiya mallakar kasar Sin.
Sanarwar ta kara da cewa, SACH ta ce a 'yan kwanakin nan an samu karin goyon baya da kuma fahimtar juna.
Mafi yawan kayayyakin tarihin gargajiya na kasar Sin da aka sace a karni na 19 da na 20, ya kasance batu mai matukar sosa rai ga al'ummar Sinawa. Kuma ci gaba da yin gwanjonsu a kasashen duniya yana matukar bakanta ran al'ummar Sin. (Ahmad Fagam)