Kazalika ana fatan gabatarwa Najeriyar karin wani jirgin sintirin nan gaba cikin wannan shekara.
Da yake karbar jirgin a madadin rundunar sojin ruwan Najeriya,Vice Admiral Usman Jibrin, ya ce jirgin zai yi matukar tallafawa sojin ruwan kasa, a fannin yaki da laifukan da suka jibanci ruwan kasar.
Jibrin ya kara da cewa akwai dadaddiyar alaka tsakanin kasar Sin da Najeriya, a fannin samarwa Najeriyar jiragen yakin ruwa.
A nasa tsokaci, karamin jakadan Sin a Najeriya Liu Kan, cewa ya yi kasar sa za ta ci gaba da inganta kyakkyawar alakar dake tsakanin ta da Najeriya.