in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani masani dan Nigeriya ya ce kokarin kasar Sin na wanzar da zaman lafiya da wadata a duniya ya burge shi
2015-09-04 13:33:31 cri

Charles Onunaiju, darektan cibiyar nazarin kasar Sin a kasar Nijeriya ya bayyana cewa, ya kalli yadda kasar Sin ta gudanar da faretin soja domin bikin cika shekaru 70 da samun nasarar yaki da maharan Japan da kuma masu nuna ra'ayin karfin tuwo, wato fascist a duniya. Haka kuma jawabin shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya burge shi sosai, inda ya bayyana aniyar kasar Sin ta yin koyi da tarihi da kuma kiyaye zaman lafiya yadda ya kamata.

Charles Onunaiju wanda ya fadi haka yayin da yake zantawa da manema labaru a Nijeriya ya ce, yanzu kasar Sin na sauke nauyi yadda ya kamata a matsayin wata babbar kasa a duniya. Ya lura da cewa Sinawa na mai da hankali kan samun bunkasuwa cikin jituwa da kuma samun ci gaba tare. Yayin da take kokarin raya tattalin arzikinta, tana kuma mai da hankali kan ba da gudummuwa wajen bunkasa tattalin arzikin duniya, abin da ya karfafa gwiwar jama'ar kasashen Afirka sosai, wadanda su ma kasashe ne maso tasowa.

Charles Onunaiju ya yi fatan cewa, ta hanyar kallon wannan faretin soja, karin jama'ar Afirka za su kara fahimtar yakin maharan Japan da jama'ar Sin suka yi, tare da kara sanin aniyar kasar Sin ta tsayawa tsayin daka kan samun ci gaba cikin lumana, sa'an nan ba za ta so ta mamaye wata kasa ba tare da kuntata mata koma ta zama barazana a gare ta ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China