Rahotanni na cewa, a kwanan baya ne wani dan gidan sarautar Katar ya gana da yarima mai jiran gado na kasar Saudiya Mohammed bin Salman Al Saud, inda ya bayyana fatansa na ganin kasar Saudiya ta baiwa 'yan Katar damar samun zuwa aiki Hajji a birnin Mekka. Daga baya kuma, sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud na Saudiya ya ba da umurnin sake bude kan iyakar kasashen biyu, wanda aka rufe sakamakon takun sakar diplomasiyya da Katar, kana ya ce zai biya kudin jigilar jiragen saman maniyatan kasar ta Katar. Ya zuwa yanzu an bude kan iyakar, kuma 'yan kasar Katar sama da 100 sun shiga kasar Saudiya ta mota don halartar aikin Hajjin. (Bilkisu)