in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya taya tawagar masu bincike murnar isa yankin Qinghai-Tibet mai tsaunuka
2017-08-20 12:32:24 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya a aike da sakon taya murna ga tawagar masana kimiyya masu bincike a yankin Qinghai-Tibet mai yawan tsaunuka.

Xi ya gabatar da wasikar taya murna da yin jinjina ga masana kimiyyar, da dalibai matasa da ma'aikata masu ba da taimako wadanda za su gudanar da bincike karo na biyu a yankin mai yawan tsaunuka.

Shugaba Xi ya ce, ya kamata su mayar da hankali game da matsalolin da suka shafi albarkatu da yanayin muhalli, da barazanar ibtila'i da kuma ci gaban yanayin tsirrai na yankin mai yawan tsaunuka.

Yankin na Qinghai-Tibet mai tsaunuka, wani muhimmin waje ne game da sha'anin muhallin halittu, kuma yanki ne dake da dubun albarkatu dake jibge a karkashin kasa, in ji wasikar ta shugaba Xi ya aike da ita.

Shugaban na Sin ya ce, ziyarar masana kimiyyar za ta kara bunkasa ci gaban yankin mai fama da tsaunuka, wanda kuma shi ne yankin dake ba da kariya ga muhallin halittu mafi girma a duniya.

A shekarar 1970 ne kasar Sin ta fara tura tawagar masana kimiyya zuwa yankin mai yawan tsaunuka.

An samu nasarar tattara wasu kayayyaki masu yawa, wadanda su ne ginshikan da masana kimiyyar suka yi amfani da su wajen gina aikin bincikensu na tattalin arziki da ci gaban zamantakewa da kuma na kula da muhalli a yankin baki daya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China