in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya bukaci matasa da su yi kokarin fahimtar tushen kasa domin samar da ci gaba
2017-08-15 19:06:32 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci matasan kasar sa da su rika shiga harkokin al'umma a matakin farko, domin fadada fahimtar su game da yanayin kasar da al'ummar ta, su kuma yi amfani da kwazon su wajen kirkiro sabbin abubuwa, da sana'o'i masu alfanu ga kasa.

Shugaban na Sin wanda ya bayyana hakan cikin wata wasika ta martani, ga sakon wani dalibi da ya shiga shirin kirkirar sana'o'i, karo na uku na kasar Sin mai lakabin "Internet Plus", ya ce yana fatan dalibai za su karfafa zukatan su, su kuma zage damtse wajen cimma burikan da kasar su ta sanya gaba.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China