in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya aikewa al-Sisi sakon ta'aziyyar hadarin jirgin kasa da ya hallaka mutane a kasar
2017-08-13 12:11:30 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon ta'aziyya ga takwaransa Abdel-Fattah al-Sisi, na kasar Masar, bisa rasuwar mutane 49 a kasar ta arewacin Afrika, sakamkon mummunan hadarin jirgin kasa.

A sakon da Xi ya aikawa al-Sisi, shugaban na Sin ya ce yayi matukar kaduwa bisa samun labarin aukuwar hadarin jirgin kasan da ya faru a kusa da birnin Alexandria, lamarin da ya haddasa hasarar rayuka masu yawa.

Xi, a madadin gwamnatin kasar Sin da al'ummar Sinawa, da kuma a madadin kashin kansa, ya nuna juyayi gami da yin ta'aziyya ga iyalan wadanda hadarin ya rutsa da su tare da yin fatar samun sauki ga wadanda suka samu raunuka a hadarin.

Idan za'a iya tunawa, da safiyar ranar Jumma'a ne jirgin kasan Masar wanda ya taso daga birnin Al-kahira wanda ke hanyarsa ta zuwa birnin Alexandria ya yi karo da wani jirgin da ya taso daga birnin Port Said, inda ya hallaka mutane 49, wasu mutane sama da 100 suka jikkata.

Shugaban kasar al- Sisi ya bukaci a hanzarta inganta fannin sufurin jiragen kasa domin kaucewa munanan hasarar rayukan jama'a.

Shugaban kasar ta Masar Abdel-Fattah al-Sisi ya yi wannan kiran ne a ranar Asabar, cikin wata sanarwa da mai Magana da yawunsa ya fitar, ya nanata muhimmancin inganta fannin sufurin domin kaucewa hadduran jiragen kasan, wanda ke haddasa hasarar rayuka masu yawa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China