A yau Alhamis ne shugana kasar Sin Xi Jinping, ya gana da babban shugaban rundunonin sojojin Amurka Janar Joseph Dunford, a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing.
Yayin zantawar su, shugaba Xi ya bayyana Janar Dunford, a matsayin babban jami'in rundunar sojojin Amurka na farko da ya kawo ziyara nan kasar Sin, tun bayan da shugaba Donald Trump ya dare karagar mulkin kasar ta Amurka.
Ya ce duk da cewa ziyarar yar takaitacciya ce, tana da cikakkiyar ma'ana, ta kuma shaida cewa an samu ci gaba mai gamsarwa, game da kyakkyawar alakar dake tsakanin rundunonin sojin kasashen biyu.(Saminu Alhassan)