Kasar Sin za ta inganta harkokin kiwon lafiya da kula da tsoffi
Kasar Sin na kokarin inganta kiwon lafiya da kula da tsoffi ta hanyar karfafa amfani da karin dabarun kula da lafiya da cibiyoyin kula da tsoffi.
Shugaban hukumar kula da lafiya da tsarin kayyade iyali na kasar Sin Wang Haidong ne ya bayyana haka, yayin ganawa da manema labarai kan tsare-tsaren kula da tsoffi, da majalisar gudanarwar kasar ta wallafa a farkon watan Yuni.
Manufar kasar Sin ita ce, a bana, asibitocinta sama da kashi 80 su tanadi hanyoyin na musammam da tsoffi za su rika bi idan suna son ganin likita domin kula da lafiyarsu cikin sauki, yayin da kuma sama da cibiyoyin kula da tsoffin 50 za su kara inganta ayyukansu na kula da lafiya.
Bugu da kari, Likitocin iyali za su rika ba da tsoffi fifiko, inda ake sa ran tsoffin za su rika samun kula ta musammam.
Manufar ita ce, ya zuwa karshen 2017, kashi 60 na tsoffi a kasar Sin, za su samu likitocinsu na musammam. (Fa’iza Mustapha)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku