in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta zama kasa ta biyu a duniya da ta fi amfani da magunguna
2017-07-13 10:41:34 cri

Mataimakin Daraktan hukumar kula da inganci abinci da magunguna ta kasar Sin Wu Zhen, ya ce kasar Sin ta zama kasa ta biyu a duniya da ta fi amfani da magunguna, haka zalika ita ce ta fi ko wacce kasa a duniya fitar da magunguna zuwa kasashen waje.

A cewar Wu Zhen, kudin shiga da kamfanonin kasar 5,000 masu hada magunguna ke samu ya kai yuan triliyan 2.5, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 370.

Kusan kamfanonin hada magunguna 50 ne suka samu tantancewa a Turai da Amurka, kuma yawan kayayakin da suke fitarwa ya haura dala biliyan 13.5.

Wu ya ce kwalliya ta biya kudin sabulu, game da kokarin hukumar na gaggauta aiwatar da ayyukan sahalewa sabbin magunguna tare da kammala sauran ayyukan da suka taru. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China