Rundunar 'yan sandan Burkina-faso ta sanar da cewa, an kai hari da bindigogi a kan wani titi dake tsakiyar birnin Ouagadougou, sai dai sojojin tsaro sun riga sun isa wurin, kana sun killace yankunan dake dab da wurin. Haka kuma 'yan sandan sun yi kira ga mazauna wurin da su kai zuciya nesa, su kuma zauna a gidajensu, kana su nisanci wuraren dake kusa da tsakiyar birnin.
Wasu mazauna wurin sun ce, an kai farmakin ne a wani dakin shan kofi dake kan titin, kana an ji karar bindiga da abubuwan fashewa a duk tsawon daren ranar, sai dai har yanzu jami'an tsaro sun killace wurin.
Kasar Burkina Faso dake yammacin nahiyar Afirka ta yi iyaka da kasar Mali daga bangaren arewacin kasar, kana a 'yan shekarun kasar ta fuskantar harin ta'addanci. (Bilkisu)