in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fasahar kasar Sin ta rage talauci tana amfanawa kasashen Afirka, in ji masanin Afirka
2017-06-20 19:24:06 cri

Nan gaba kadan za a shirya taron yayata wani littafi mai suna "fita daga talauci" wanda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya rubuta, taron da zai gudana tare da na dandalin kwararru da masana na kasashen Sin da Afirka karo na 6, tsakanin ranekun 21 zuwa 22 ga watan nan a birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha.

Ana sa ran yayin taron, za a tattauna kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka dangane da rage talauci, da samun ci gaba mai dorewa a Afirka. Kafin taron, shehun malami Innocent Shoo na kwalejin huldar kasa da kasa da harkokin diflomasiyyar kasar Tanzaniya, ya bayyana wa wakiliyarmu cewa, a shekarun baya, wasu karin kasashen Afirka sun gano man fetur, da iskar gas, da sauran dimbin ma'adanai. A hannu guda kuma kyawawan fasahohin kasar Sin na raya kasa suna da muhimmiyar ma'ana, wajen cin gajiyar wadannan ma'adanai, ta yadda jama'ar Afirkan za su amfana daga alherai dake tattare da hakan. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China