in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 9 sun rasa ransu sakamakon girgizar kasa a lardin Sichuan
2017-08-09 09:17:43 cri

Kawo yanzu mahukuntan lardin Sichuan na kasar Sin, sun tabbatar da rasuwar mutane 9, tare da jikkatar wasu 164, sakamakon girgizar kasa mai karfin maki 7.0, wadda ta auku a garin Zhangzha dake gundumar Jiuzhaigou a daren jiya Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa, biyar daga wadanda suka rasu baki ne 'yan yawon bude ido, wadanda ke ziyartar tsaunukan Jiuzhaigou masu koramu da 'yan yawon shakatawa ke matukar sha'awar ziyarta.

Tuni dai shugaban kasar Sin Xi Jinping da firaministan kasar Li Keqiang, suka ba da umarnin hanzarta daukar dukkanin matakan da suka wajaba na tallafin jin kai, a yankin da wannan bala'i ya auku.

An ce, yawan mutane da suka ziyarci koramun Jiuzhaigou a jiya Talatar ya kai kimanin 34,000. Tuni kuma aka debe masu ziyara 31,000 daga yankin zuwa wuri maras hadari, yayin da aka gyara hanyoyin sadarwa da na makamashi, da layukan ruwa da suka lalace sakamakon ibtila'in. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China