in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Girgizar kasa ta auku a yankin Xinjiang
2017-08-09 10:46:20 cri

Da sanyin safiyar yau Laraba ne wata girgizar kasa mai karfin maki 6.6, ta girgiza gundumar Jinghe a yankin Bortala da ke jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta a arewa maso yammacin kasar Sin.

Hukumar dake lura da girgizar kasa ta kasar Sin CENC ta tabbatar da aukuwar bala'in, tana mai cewa, al'ummun birnin Urumqi, da Karamay da Yining dake da nisan kilomita 400 zuwa 200, sun ji tasirin girgizar kasar.

Gundumar Jinghe dai na da yawan al'umma kimanin mutum 140,000.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China