in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin da nahiyar Afrika za su karfafa hadin gwiwa da kirkire-kirkire a kan makamashi mai tsafta
2017-08-08 10:10:45 cri
An kaddamar da wani shirin kawance kan makamashin da ake sabuntawa da kirkire-kirkire jiya Litinin a nan birnin Beijing, tsakanin kasar Sin da nahiyar Afrika, domin bunkasa hadin gwiwa tsakaninsu kan makamashi mai tsafta.

Mambobin shirin kawancen sun hada da cibiyoyin hada-hadar kudi da masu samar da kayayyaki da masu sayar da lantarki ta na'ura da kuma manyan masu sarrafa kayayyaki ta hanyar amfani da makamashi mai tsafta.

A cewar wani tsarin ci gaba mai dorewa, shirin zai taimaka wajen samar da lantarki tare da tsarin rarrabawa a Afrika ta hanyar ayyukan hadin gwiwa tsakanin gwamnatoci da bangarori masu zaman kansu.

Jami'ar gamayyar kungiyar cibiyoyin bincike da kamfanoni da jami'o'i na kasar Sin Ding Yuxian, ta ce kawancen zai bunkasa harkokin makamshi mai tsafta.

Ding Yuxian ta kara da cewa fadada aiwatar da tsare-tsaren kasar Sin a Afrika zai bunkasa amfani da makamashi mai tsafta a kasar Sin da nahiyar Afrika.

A nasa bangaren, jakadan Jamhuriyar Benin a kasar Sin Simon Pierre Adovelande, cewa ya yi, akwai bukatar bangarorin su hada jari da albarkatu, yana mai cewa kawancen dandali ne da ya dace da yin hakan.

Ya ba da shawarar shirin ya fara da wasu ayyuka kafin a fadada shi zuwa fadin Afrika. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China