Ministan kimiyya da fasaha na kasar Ogbonnaya Onu, ya sanar a jiya bayan kammala taron majalisar zartaswar kasar cewa, sabon shirin zai taimaka wajen koyar da fasaha tare da samun karin kudin haraji da kuma arziki ga kasar da al'ummarta.
Ogbonnaya Onu ya ce daga cikin kunshin shirin, kamfanonin dake sarrafa manyan kayayyakin da Nijeriya ke saye tare da odarsu daga kasashen ketare, za su je kasar su kafa kamfanoninsu domin su rika sarrafa irin kayayyakin a can.
Ya ce yin hakan zai samar da aikin yi ga jama'a, sannan gwamnati za ta rika karbar kudin haraji daga kamfanonin wanda zai kara mata arziki, amma kuma abu mafi muhimmanci shi ne, Nijeriya za ta koyi ayyukan fasaha da za su taimaka wajen inganta kwarewarta.
Ministan ya ce manufar ita ce, cikin shekaru 10 masu zuwa, masana'antun Nijeriya su iya gudanar da manyan ayyuka, musamman wadanda ba su da kwarewa a kai a yanzu.
Har ila yau, Ogbonnaya Onu ya shaidawa manema labarai cewa, ta wannan hanya ce kadai Nijeriya za ta koyi ayyukan fasaha da take bukata domin bunkasa kwarewarta, yana mai fatan cewa nan da shekaru 20 masu zuwa kamfanonin kasar za su iya takara da wadanda suka fi kowanne a duniya. (Fa'iza Mustapha)