Masharhanta dai na ganin Xu Lijia, na da zarafin shiga a dama da ita a gasar shekarar 2020 ta birnin Tokyo, kasancewar ana sa ran kafin lokacin za ta murmure daga ciwon da ta ji a kafada, wanda kuma shi ne zai hana ta shiga gasar dake tafe a Tianjin.
Wasu hotunan da aka wallafa kan shafin sada zumunta na Weibo sun nuna Xu, sanye da kayan masu jinya, tana murmushi kafadar ta ta hagu na daure, kana ta dama nannade da bandeji, ta daga dan yatsanta guda a matsayin jinjina.
Wata guda kafin fara gasar Olympic ta birnin Rio da aka gudanar a shekarar 2016 ne Xu ta fara jin ciwo a kafadar ta, amma duk da haka sai da ta kammala wasannin wannan gasa. Daga nan ne kuma likitocin ta suka ba ta shawarar yin hutu har tsawon watanni 6, kana aka yi mata aiki a kafadar hagu.
Da take bayyana halin da take ciki, Xu ta ce za ta shafe watanni 6 tana jiyya, daga nan kuma ta fara shirin fuskantar gasar Olympic ta gaba.
A shekarar 2014, Xu ta zama daya daga alkalan wasan tseren kwale kwale na duniya, kuma mamba a kwamitin hukumar dake lura da wasan ta duniya. A hannu guda kuma 'yar wasan, na ci gaba da karatun digiri na biyu a kasar Birtaniya. Karatun da ta bayyana a matsayin wata babbar dama ta cimma burin samun dinbin ilimi.
Har wa yau Xu na da burin kafa wata kungiyar 'yan wasan tseren kwale kwale daga garin ta na haihuwa, wanda wannan buri ya haifar da kasancewar ta jakada, kuma mai horas da 'yan wasan "China One Ningbo", tawagar da tuni ta lashe gasar M32 ta kasa da kasa da aka gudanar a kasar Sweden.
Burin Xu da sauran masu ruwa da tsaki dai shi ne, ganin tawagar ta "China One Ningbo" ta zamo jigon kafuwar wannan wasa a zukatun Sinawa, tare da kara karfafawa masu sha'awar sa gwiwar shiga a dama da su, kamar dai yadda daya daga abokan aikin ta Sun Xiao ya bayyana.
Yayin da wasu ke kallon wasan tseren kwale kwale a matsayin wasa na masu hali, a hannu guda Xu, ta ce bata amince da wannan ra'ayi ba, domin kuwa a cewar ta, ta fara koyon fasahar wasan ne cikin kwale kwale da bai wuce kudin Sin RMB 10,000 ba. Don haka ta shawarci masu sha'awar wasan da su fara da matakin kungiyoyi, kafin su yi karfin mallakar kwale kwalen na kashin kan su.
Ta ce ba banbanci tsakanin maza da mata, ko banbancin shekaru, ko tsawo ko kudin shiga, akwai nau'oin kwale kwale daban daban da mai sha'awar wasan ka iya mallaka domin amfani da shi gwargwadon bukata.
Wasan tseren kwale kwale dai na da farin jini sosai a nan kasar Sin, inda al'ummar kasar ke nuna goyon bayan su matuka ga ci gaban sa.(Saminu Alhassan)