in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Salon wasa da kwallon kafa
2017-07-30 09:37:00 cri


An fara salon wasa da kwallo wato Freestyle football a wasu kasashen dake nahiyar Latin Amurka, wato Amurka ta Kudu ke nan, a shekarun 1990s. A da, an fi samun yara dake wannan wasa ne cikin ugwannin matalauta, inda yara ke sha'awar kwallo kafa, amma watakila ba su da filin buga wasan, saboda haka sukan fara gasa a tsakaninsu kan fasahar sarrafa kwallo. Ta haka, duk da cewa ba su da filin wasa, amma suna iya wasa da kwallo bisa kwarewa.

Amma ba a fara yayata wasan zuwa sauran sassan duniya ba tukuna, sai bayan da kamfanin Nike ya kaddamar da shirye-shiryen yada wasan a shekarar 2000, kuma wasu masu sha'awar wasa sun fara sanya bidiyonsu kan tashar Internet ta Youtube, domin karin mutane su samu damar ganin yadda ake wannan salon wasa da kwallo.

A lokacin kamfanin Nike ya yi tallace-tallace da bidiyon wasan Freestyle football, bidiyon da ake kiransa "Joga Bonito", wato "Nuna fasahohi masu kyan gani" a Hausance. A cikin tallace-tallacen bidiyon, shahararrun 'yan wasan kwallon kafa, irinsu Ronaldinho, Cristiano Ronaldo da Edgar Davids, sun nuna fasahohinsu, lamarin da ya janyo hankalin jama'a na kasashe daban daban. A kan alakanta tallace-tallacen da aka nuna a wanna karo, da yadda salon wasa da kwallon kafa ya fara farin jini a duniya.

Daga bisani, bisa amfani da tashar internet ta Youtube, inda masu sha'awar wasan freestyle football suke iya daukar bidiyon yadda suke wasa, sa'an nan su sanya bidiyon kan shafin internet, mutane da yawa sun fara shahara, dalilin kwarewarsu a fannin wasan freestyle football. Hakan ma ya kara janyo hankalin jama'ar duniya, musamman ma matasa, cikin salon wasa da kwallon kafa.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China