in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Iraki za su kwato Mosul daga hannun IS cikin kwanaki biyu
2017-07-05 10:23:32 cri
Kwamandan sojojin kasar Iraki manjo-janar Najim al-Jubouri, ya lashi takwabin cewa, dakarunsa za su kwato baki dayan birnin Mosul daga hannun mayakan IS cikin kwanaki biyu.

Manjo-janar Najim wanda ya bayyana hakan cikin wata sanrwa da aka rabawa manema labarai, ya ce yanzu haka dakarun na shirin nausawa zuwa wuri na karshe dake hannun mayakan na IS wato Tal Afar a lardin Nineveh. A cewarsa mitoci 400 ne kacal suka rage a hannun 'yan tawayen a fafatawar da ake yi a bangaren yammacin tsohon birnin Mosul. Kuma da zarar sun yi nasarar kwace garin al-Maydan, za a sanar da kwato yankunan dake yammacin bakin kogin Tigris baki daya.

Dakarun dake yaki da ayyukan ta'addanci na Iraki, da sojoji, 'yan sanda gami da dakarun kai daukin gaggauwa sun shafe tsawon lokacin suna fafatawa da mayakan na IS a tsohon birnin Mosul, amma yakin na tafiyar hawaniya sakamakon turjiyar da mayakan ke nunawa.

Tun a watan Yunin shekarar 2014 ne dai sassa da dama na lardin Nineveh ciki har da Mosul, babban birnin yanki suka fada hannun mayakan IS, lokacin da dakarun gwamnati suka gudu suka bar makamansu, lamarin da ya baiwa IS din kwace iko da yankunan arewaci da yammacin kasar ta Iraki. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China