in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar tsaron kasar Sin ta gudanar da liyafar murnar cika shekaru 90 da kafuwar PLA
2017-08-01 11:39:13 cri
Ma'aikatar tsaron kasar Sin ta gudanar da liyafar murnar cika shekaru 90 da kafuwar sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin PLA, jiya Litinin a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing.

Yayin liyafar, mamban kwamitin tsakiya mai kula da harkokin sojan kasar Sin, kuma mamban majalisar gudanarwar kasar kana ministan tsaron kasar, janar Chang Wanquan ya bayyana cewa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ce ta kafa tare da jagorantar sojojin 'yantar da jama'ar kasar PLA, da taka muhimmiyar rawa a sha'anin raya kasa da yin kwaskwarima a kasar.

Chang Wanquan ya ce a cikin shekaru 90 da suka gabata, sojojin PLA sun sauke nauyin da ke wuyansu na wanzar da zaman lafiya da tabbatar da adalci da kuma nuna karfi.

Ya kara da cewa, kamata ya yi dukkan sojojin PLA su martaba manufofin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wadda ke karkashin jagorancin Xi Jinping, da akidojin Mao Zedong da na Deng Xiaoping.

Sannan su mai da hankali kan munufofi 3 na jam'iyyar kwaminis ta Sin ta fuskar samar da kayayyaki, da raya makomar al'adu na zamani, da kuma moriyar jama'ar kasar Sin.

Sauran sun hada da inganta samun bunkasa bisa amfani da kimiyya da fasaha, da kuma tunanin jawabin shugaba Xi Jinping da sabbin manufofin raya kasa da gudanar da harkokin siyasa, da ayyukan domin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da jama'ar kasar, don maraba da gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 19 da za a yi a karshen shekarar bana. (Zainab Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China