in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi bikin faretin murnar cika shekaru 90 da kafuwar PLA
2017-07-30 09:17:41 cri

Ranar 1 ga watan Agusta, rana ce ta cika shekaru 90 da kafuwar rundunar 'yantar da jama'ar kasar Sin ta PLA, domin taya murna ta wannan muhimmiyar rana, da karfe 9 na safiyar yau, an yi bikin fareti a sansanin horaswa dake garin Zhurihe na jihar Mongoliya ta gida.

Haka kuma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin, inda ya gabatar da wani muhimmin jawabi. Wannan shi ne karo na farko da rundunar sojojin kasar Sin ta yi faretin yake-yake a sarari, kuma karo na farko da aka yi faretin domin taya murnar ranar kafuwar PLA, da kuma karo na farko da aka yi faretin tun bayan da aka fara aiwatar da kwaskwarima kan tsarin kiyaye tsaron kasa, da kuma rundunar sojojin kasar ta Sin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China