Xi, wanda shi ne babban sakataren jam'iyyar kwaminis na kasar Sin CPC, kana shugaban kwamitin tsakiya mai kula da harkokin soja na kasar, ya gabatar da muhimmin jawabi bayan duba babban faretin sojojin kasar da aka gudanar a sansanin horaswa na Zhurihe dake yankin arewacin Mongoliya ta gida mai cin gashin kai a lokacin bikin murnar cika shekaru 90 da kafuwar PLA, wanda ya fado a ranar 1 ga watan Augasta.
Wannan shi ne karo na farko da kasar Sin ta gudanar da bikin ranar PLA tare da gudanar da faretin soji, tun lokacin kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin a shekarar 1949. (Ahmad Fagam)