in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An nuna wasu sabbin kayayyakin soja a yayin bikin faretin murnar cika shekaru 90 da kafuwar PLA
2017-07-30 11:09:17 cri

A safiyar yau, an yi bikin faretin murnar cika shekaru 90 da kafuwar rundunar 'yantar da jama'ar kasar Sin ta PLA a sansanin horaswa dake garin Zhurihe na jihar Mongoliya ta gida. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin, inda kuma ya gabatar da wani muhimmin jawabi.

Wannan shi ne karo na farko da aka yi fareti domin taya murnar ranar kafuwar PLA, an kuma gudanar da faretin yake-yake a sarari.

Gaba daya akwai sojoji sama da dubu goma da suka halarci bikin, yayin da jiragen saman soja guda 129, da kuma kayayyakin soja guda 571. Haka zalika, an nuna wasu sabbin kayayyakin soja a yayin bikin, wadanda kashi 40 bisa dari daga cikinsu ne karo na farko da aka nuna musu a fili.

Bayan faretin, sojojin sun taru a gaban babban dandalin duba fareti domin sauraron muhimmin jawabin na shugaban kasar Sin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China