in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyun gama kai a yankunan karkarar kasar Sin sun samu riba a watanni shida na farkon shekarar 2017
2017-07-18 10:57:42 cri
Rahotanni daga kasar Sin na nuna cewa,jam'iyyun gama kai dake yankunan karkarar kasar sun samu karuwar harkokin saye da sayarwa a watanni shida na farkon shekarar 2017 da muke ciki. Wannan nasara ta samu ne sakamakon matakan gyare-gyare da ake aiwatarwa a wannan fanni, matakin da ya baiwa mazauna yankunan karkara amfana daga gare su yadda ya kamata.

Majalisar kula da harkokin saye da sayarwar jam'iyyun gama kai ta kasar Sin, ta ce yawan kudaden da jam'iyyun gama kan suka samu a fannin sayar da kayayyaki a fadin kasar ya kai Yuan triliyan 2.35 kwatankwacin dala biliyan 347.8, adadin da ya karu da kimanin kaso 14.4 cikin 100 bisa makamancin lokacin na bara.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China