Bayyana muhimman bayanan jama'a dai ya sabawa dokar kasa, kuma aya ta 111 ta dokar kasar Sin ta bayyana cewa, wajibi ne a kare muhimman bayanan jama'a dake zaune a cikin kasar gami da hakkokinsu kamar yadda doka ta tanada.
A watan Mayun wannan shekara ce dai, kotunan kasar Sin suka yanke wani hukunci mai tsauri, dake cewa, duk wadanda aka kama da samu ko sayar da muhimman bayanai 500 ko sama za su fuskanci daurin da ya kai shekaru 7 a gidan yari.(Ibrahim)