Kwamfanonin kasar Sin sama da 3,900 sun zuba jari a kasashen waje 145 da sassa daban daban na duniya daga watan Janairu zuwa watan Yuni, kamar yadda ma'aikatar kula da al'amurran ciniki ta kasar Sin ta tabbatar da hakan.
An samu raguwar ne sakamakon sauye sauyen manufofin tattalin arzikin da kasar Sin ke gudanarwa da nufin inganta shi, bisa la'akari da yanayin da ake ciki na rashin tabbas a kasashen ketare, da kuma matakan da gwamnati ke dauka domin dakile hanyoyin zuba jari marasa tabbas, in ji kakakin ma'aikatar cinikin ta Sin Gao Feng.
Gao ya ce, a tsakiyar wannan shekara, tattalin arzikin Sin na cigaba da karuwa yadda ya kamata, hakan ya karfafa gwiwar Sinawa masu zuba jari suka yanke shawarar barin jarinsu a cikin gida.
Matsalar karuwar tashe tashen hankula a kasa da kasa da shiyya, da hare haren ta'addanci da tsauraran dokokin kasuwanci a wasu kasashen duniya su ma wasu dalilai ne da suka haifar da mummunan tasiri ga aikin zuba jari a ketare a watannin shidan farkon wannan shekarar.(Ahmad Fagam)