in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harkokin zuba jarin waje na kai tsaye a kasar Sin ya karu a cikin watan Yuni
2017-07-14 10:56:05 cri
Harkokin zuba jarin waje na kai tsaye a babban yankin kasar Sin, ya karu zuwa kashi 2.3% tsakanin watan Yunin bara zuwa bana, inda ya kai Yuan biliyan 100.45 kwatankwacin dala biliyan 14.82.

Wata sanarwa da ma'aikatar cinikayya ta kasar ta fitar, ta ce an kaddamar da sabbin kamfanonin kasashen waje guda 2,894, inda ya kai kashi 14.1% daga shekarar da ta gabata.

Zuwa tsakiyar shekarar nan, jarin ya kai Yuan biliyan 441.54, wanda ya dan sauka da kashi 0.1% cikin shekara guda, yayin da adadin sabbin kamfanonin waje ya karu da kashi 12.3% zuwa 15053.

Kakakin ma'aikatar Gao Feng, ya bayyana cewa, harkokin zuba jarin na nan yadda suke ba tare da wata matsala ba cikin watannin shidan farko na shekarar nan, sannan tsarin na ci gaba samun tagomashi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China