in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fasahar jirage marasa matuka ta samar wa Najeriya damammakin tattalin arziki
2017-07-18 08:55:10 cri

Karamin ministan zirga-zirgar jiragen sama na Najeriya Hadi Sirika ya bayyana cewa, kasarsa za ta ci gajiyar damammaki ta fannin tattalin arziki daga tsarin nan na jiragen sama marasa matuka.

Da yake karin haske game da hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a Abuja, fadar mulkin kasar, ministan ya ce, karkashin wannan tsari, za a samu ribar da ta kai dala biliyan guda daga sayar da irin wadannan jirage a wannan shekara ta 2017 da kuma 2018, kuma ya zuwa yanzu an sayar da irin wadannan jirage marasa matuka miliyan hudu.

A cewarsa, tsarin yana janyo masana a fannin fasahohin kere-kere da masana'antu, kana za a iya cin gajiyar jiragen a fannoni daban-daban. Ya kuma shaidawa mahalarta taron cewa, jirage marasa matukan suna farfado da wasu fannoni kamar na aikin gona, shirya fina-finai, harkar gidaje, baya ga samar da guraben ayyukan yi, da damammaki a fannin tattalin arziki.

Ministan ya kara da cewa, irin wadannan jirage marasa matuka na gudanar da ayyukan da suka kasance masu matukar hadari ga dan-Adam ko wasu jirage dake aiki a bangaren mai da iskar gas a Najeriya.

Ya ce, yanzu haka wannan tsari na bunkasa cikin sauri a duniya, ganin yadda irin wadannan jirage marasa matuka suke kara janyo hankalun masu sha'awa da kuma masana'antu.

Hukumar kula da jirga-jirgar jiragen sama ta duniya (ICAO) tare da hadin gwiwar ma'aikatar sufuri ta tarayyar Najeriya ce suka shirya wannan taro.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China