in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwanintar Sinawa ta ja hankalin matasan Nigeriya
2015-05-25 10:02:28 cri

Cibiyar al'adu ta Sinawa dake Abuja, babban birnin tarayyar Nigeriya ta shirya wani horo na makwanni biyu a kan yanka takarda da dabarar kokwa ta Sinawa ga daliban kasar a wani kokari na inganta al'adun Sinawa.

A cikin makonni biyu, dalibai daga makarantun sakandare daga fadin birnin da suka hada da makarantun kasashen waje, masu dalibai daga Masar, Sham, Iraqi, Sudan da Morocco.

A cikin azuzuwan, malamai Fengying Wang, Lianxia Li da kuma Lining Wang daga cibiyar al'adu ta Qinghai ne suka koyar wa daliban fasahar, kuma wannan ne karonsu na farko a Nigeriya, duk da sun je Benin da wassu kasashen yammacin Afrika domin irin wannan horaswa.

An dai shirya azuzuwan ne a lokacin bikin bajen kolin al'adun Qinghai da aka fara tun daga ranar 8 zuwa 22 ga watan nan na Mayu, inda daliban suka nuna basirar da aka koyar musu, sannan su ma a nasu bangaren suka mika wa malaman kyaututtukan yabawa.

Shugaban shirin Yan Xiangdong, babban jami'in al'adu na ofishin jakadancin Sin a Nigeriya ya bayyana jin dadin shi ga yadda matasan suka halarci daukan horon, tare da fatan za su kirkiro wani abu ta hanyar hada basirar da aka koya musu da nasu al'adun na asali. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China