Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan yayin taron tawagar masu ruwa da tsaki game da tattalin arziki da cinikayya ta kasar Sin, ya kara da cewa matakin, zai saukaka ka'idojin da ake bi wajen rage wahalhalun rajistar sana'oi ta yadda za a samu karin sauki. Kaza lika shugaban na Sin ya ce burin kasar sa shi ne samar da daidaito, da adalci, da gudanar da al'amura a fayyace. Wanda hakan zai tabbatar da ci gaban Sin cikin kyakkyawan yanayi. (Saminu)