in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Halartar taron G20 da shugaba Xi ya yi ya karfafa hadin gwiwar kasa da kasa, in ji Wang Yi
2017-07-10 09:49:15 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana halartar taron kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi, a matsayin wani mataki da zai bunkasa hadin gwiwar dake akwai tsakanin kasashe mambobin kungiyar.

Mr. Wang ya ce, shugaban na Sin, da sauran shugabannin kasashen kungiyar, sun tattauna a taron na birnin Hamburg, da nufin lalubo hanyoyin wanzar da ci gaba mai dorewa, bisa tushen taron birnin Hangzhou da ya gabata a shekarar bara.

Kaza lika ministan ya ce, Sin ta ba da dukkanin gudunmawa, wajen karfafa hadin gwiwa tsakanin mambobin G20, musamman a bangarorin inganta jagoranci a fannonin raya tattalin arziki.

Har wa yau yayin taron na Hamburg, shugaba Xi ya shiga shawarwari na raya harkokin cinikayya, da kasuwanci, da hada hadar kudade, da sabon salon tattalin arziki ta hanyar amfani da fasahohin zamani.

Sauran fannonin sun hada da na inganta samar da makamashi, da batun sauyin yanayi, da samar da ci gaba, da raya nahiyar Afirka, da inganta kiwon lafiya. Har wa yau mahalarta taron sun tabo batutuwan da suka shafi 'yan gudun hijira, da na bakin haure, da batun yaki da ta'addanci, inda kuma aka fadada batu game da ra'ayin kasar Sin don gane da dabarun warware matsalolin da duniya ke fuskanta, da ma nacewa ingantaccen salon hadin gwiwar kasa da kasa da Sin din ke tunkaho da shi.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China