in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya jaddada muhimmancin raya harkokin kudi
2017-07-16 13:28:14 cri
An yi babban taron harkokin hada-hadar kudi na kasar Sin daga ranar 14 zuwa 15 ga wata a birnin Beijing. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron, inda ya gabatar da jawabin dake cewa, hada-hadar kudi gami da tattalin arziki, muhimmin karfi ne na wata kasa, kana, tsaron kudi na daya daga cikin harkokin tsaro na kowace kasa.

Xi ya jaddada cewa, a 'yan shekarun nan, harkokin kudi da tattalin arziki na kasar Sin na samun ci gaba da wasu manyan nasarori, kuma kasar na nuna himma da kwazo wajen yin garambawul ga harkokin kudi gami da kyautata tsarinsa.

Shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, muddin ana son gudanar da harkokin kudi da tattalin arziki yadda ya kamata, dole a bi wasu ka'idoji wadanda suka hada da, inganta harkokin bada hidima ta fuskar kudi da tattalin arziki, ta yadda za'a iya biyan bukatun jama'a. Da kyautata tsarin hada-hadar kudi da kasuwar kudade, da kuma daidaita bunkasuwar sha'anin kudi da ci gaban zaman rayuwar al'umma. Sannan ya ce karfafa sa ido gami da kara karfin shawo kan zai iya kunno kai ta fannin harkokin kudi. Bugu da kari ya ce kamata ya yi kasuwanni su kara taka rawarsu ta fannin daidaita harkokin kudade, da kuma daidaita dangantaka tsakanin gwamnati da kasuwanni.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China