in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 4 sun mutu a sanadiyyar wani hari a arewacin Najeriya
2017-07-16 12:50:11 cri
Wani babban jami'i a jahar Kaduna dake arewacin Najeriya ya bayyana cewa wasu 'yan bindiga da ba'a san ko suwanene ba sun kashe Fulani makiyaya 4 a jahar.

Mai Magana da yawun kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta Najeriya Abdullahi Ibrahim, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan da aka yi garkuwa da fulanin biyu a yankin Kajuru dake jahar Kaduna.

Ibrahim ya kara da cewa, maharan sun kuma afkawa al'ummar yankin Chikun dake jahar inda suka lalata gidaje masu yawan gaske.

Ya bukaci al'ummar yankunan da su kwantar da hankalinsu, kana ya bukaci hukumomin tsaro da su maida hankali wajen binciko wadanda suka aikata laifukan.

Ya zuwa yanzu hukumomin 'yan sandan yankin ba su tabbatar da faruwar al'amarin ba.

Yawan kone kone, da kasheshen rayukan mutanen da basu ji ba basu gani ba wanda ake zargin Fulani da aikatawa yana neman zama ruwan dare a yankin kudancin jahar Kaduna musamman a 'yan kwanakin da suka gabata.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China