in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Ruwan Nijeriya sun dakile yunkurin fashin wani jirgin ruwa
2017-07-15 12:25:56 cri
Sojojin ruwa a Nijeriya, sun yi nasarar dakile yunkurin fashin wani jirgin ruwa mai dauke da kayakin sayarwa a yankin Bony na jihar Rivers mai arzikin mai dake kudancin kasar.

Kakakin rundunar sojin ruwan Capt. Suleiman Dahun, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua jiya a Abuja, fadar mulkin kasar cewa, al'amarin ya auku ne a ranar Alhamis da ta gabata.

Suleiman Dahun ya ce mutane 6 da ake zargi sun hau jirgin, sai dai sun gaza isa inda matuka ke zama da kuma dakin injin jirgin, domin matukan sun kulle ko ina.

Ya kara da cewa, da ganin kwale kwalen sintiri na soji, sai barayin suka tsere ba tare da aiwatar da nufin nasu ba.

Ya ce binciken farko-farko ya bayyana cewa, babu wani matuki da aka sace, haka zalika babu wani abu da aka dauka. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China