Rundunar ta NAF ta ce a shekarar 2013 aka fara aiwatar da wannan horo, amma daga baya aka dakatar saboda karancin kayan gyaran nau'in wadannan jirage, kafin kuma yanzu a sake bude gudanar da shi.
Da yaka karin haske game da hakan, yayin kaddamar da bada horon a jihar Kaduna dake arewacin Najeriya, babban jami'i mai lura da tsare tsare AVM Iliyasu Muhammad, ya ce cibiyar bincike da samar da ci gaba ta rundunar, ta riga ta samar da managarcin tsarin ba da wannan horo, a wani mataki na tabbatar da dorewar sa. Za kuma a fara ne da horas da dakaru 5 cikin watanni 3.(Saminu Alhassan)