Okorafor ya ce lalata talardun Naira tamkar wulakanta kimar kasar ne. Kana ya bayyana damuwar sa game da yadda wasu 'yan kasar ke watsi, tare da tattaka takardun kudin kasar a wuraren bukukuwa wanda hakan ke sanyawa su lalace.
Jami'in na babban bankin Najeriya ya kara da cewa, a halin da ake ciki sun dukufa wajen wayar da kan al'umma a sassan kasar daban daban, hanyoyin da za su gane takardun Naira na jabu, da yadda za su rike kudi ba tare da sun lalata su ba.
Ya ce bai dace a rika rubutu kan takardun na Naira ba, haka kuma ya zama wajibi a kaucewa sanya masu datti ko yamutse su.(Saminu Alhassan)