Shugaban majalisar ba da shawara kan harkokinn siyasa na kasar Sin Yu Zhengsheng ya bayyana cewa, kasashen Sin da Equatorial Guinea za su kara yin hadin gwiwa karkashin shawarar ziri daya da hanya daya.
Mr. Yu wanda har ila yau shi ne shugaban kwamitin taron tuntuba game da harkokin siyasa na kasar Sin, ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da mataimakin shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Nguema Obiang Mangue.
A nasa jawabin Mangue ya yaba wa kasar Sin bisa taimakon da ta dade tana baiwa kasarsa. Kana a shirye kasarsa take ta kara zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin ta yadda hakan zai amfana wa al'ummomin kasashen biyu. (Ibrahim)