Tsarin dai ya samu amincewa ne a zaman kwamitin da ya gudana a jiya Laraba, karkashin jagorancin firaministan kasar Li Keqiang.
Karkashin wannan tsari, Sin za ta samar da hadadden salo na yin rajistar sana'o'i mai sauki ga baki, da ma 'yan kasar ta Sin. Kaza lika gwamnatin kasar za ta fidda hanyoyin samun takardun zama ga baki wadanda ke da matukar hazaka, kuma ke son kafa sana'o'i masu alaka da samar da gidaje, da makarantu, da fannin kula da lafiya.
Har ila yau karkashin tsarin, dalibai 'yan kasashen waje da suka kammala karatun su a nan kasar Sin, na iya amfani da takardun karatun su wajen neman izinin zama a kasar don gudanar da sana'o'i.(Saminu Alhassan)