in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Osinbajo: Shugaba Buhari yana samun sauki sosai
2017-07-12 19:41:46 cri

Mukaddashin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya bayyana cewa, shugaba Muhammadu Buhari dake jinya a Burtaniya yana samun sauki sosai, kuma nan ba da dadewa ba zai dawo gida.

Osinbajo ya bayyana hakan ne ga manema labarai yau da safe a Abuja, fadar mulkin kasar, kafin ya jagoranci taron majalisar zartarwar kasar.

A jiya ne dai Osinbajo ya yi tattaki zuwa Burtaniya don ya gana da Buhari. Tun a ranar 7 ga watan Mayu ne Buhari ya bar Najeriya zuwa Burtaniya don likitocinsa su duba lafiyarsa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China