in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jagoran IEA ya jinjinawa Sin game da aikin hakar sabon nau'in iskar gas mai matukar amfani
2017-07-12 11:03:02 cri
Babban daraktan hukumar makamashi ta kasa da kasa IEA, Mr. Fatih Birol, ya jinjinawa kokarin kasar Sin game da aikin hakar sabon makamashin iskar gas na hydrates daga teku.

Mr. Birol ya ce Sin ta shiga gaba, a fannin aiwatar da bincike da raya makamashi ta hanyar amfani da iska da hasken rana, ita ce kuma ta daya wajen cin gajiya daga makamashin nukiliya.

Jami'in ya ce aikin da Sin ta gudanar ya haifar da wani sabon sauyi a fannin samar da albarkatun iskar gas, yayin da ake dada gano sabbin dabaru, da cin gajiyar nau'oin iskar gas daban daban a sassan duniya.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai Sin ta kammala aikin fidda iskar gas rukunin hydrates, mai dauke da kaso mai yawa na iskar gas nau'in methane, a aikin gwaji da aka kwashe kwanaki 60 ana gudanarwa.

Wannan aikin dai ya zamo wani ginshiki na gudanar da karin bincike, an kuma bayyana cewa, yayin gwajin an hako sama da kubik mita 300,000 na iskar gas din nau'in methane, wadda ke kunshe da iskar gas mai tsafta da yawan ta ya kai kubik mita 5,000. Adadin da ya nuna cewa a kullum an yi nasarar hakar adadin da bai gaza kubik mita 35,000 ba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China