Kasashen da suka fi yawan baligai dake shirin fita ci rani sun hada da Najeriya, Indiya da demokradiyyar Congo, kuma kasashen da suka fi daukar hankulan masu fita ciranin sun hada da Amurka sai Birtaniya dake bi mata baya, sai kuma kasashen Saudi Arabia, Faransa, Canada, Jamus da Afrika ta kudu.
Rahoton ya ce, baligai da kan shirya tafiya ci-ranin galibinsu maza ne, samari matasa marasa aure, wadanda ke zaune a manyan birane kuma galibinsu matakin karatunsu bai wuce sakandare ba. (Ahmad)