Kakakin sojojin Ayoub Qassem, ya shaidawa kamfanin dillancin labarun Xin Hua cewa, bakin hauren da aka ceto a jiya Jumma'a, sun hada da mata 98 da yara 25, yawancinsu kuma sun fito daga kasashen Larabawa da kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara, inda suka yi shirin zarcewa Turai, amma sai jirgin ruwan su ya samu matsala.
Hukumar kula da harkokin bakin haure ta duniya ta bayyana a wannan rana cewa, tun daga farkon shekarar nan, an ceto bakin haure sama da 9,000 a yankin tekun Libya.
Tun bayan shekarar 2011 ne aka samu tabarbarewar tsaro a kasar Libya, al'amarin da ya sa gwamnatin kasar ba ta iya gudanar da harkokin bakin teku.
Kuma wannan ne ya sa wasu bakin haure da suka fito daga kasashen Afirka dake kudu da Sahara mai da Libya wata hanya ta tsallake Bahar Rum domin zuwa Turai. (Bilkisu)