Liu Jeiyi wanda shi ne wakilin din din din a MDD mai wakilai 15 yayi wannan kiran ne a taron kwamitin tsaro bayan da aka amince da shawarar daukan matakai na hana safaran mutane da jigilar bakin haure ta kan bahar Rum da ya ratsa ta Libya.
A cewar wani rahoton da ofishin kula da 'yan gudun hijira na MDD ya zuwa watan Agustan wannan shekarar kawai yan gudun hijira da bakin haure da suka tsallake bahar Rum sun wuce 300,000. Wadansu 2,500 kuma a cewar rahoton da suka hada da bakin hauren da 'yan gudun hijira da ma 'wassu daga kasar ta Libya sun mutu ko sun bace a kokarin da suke yi na tsallakawa zuwa yankin Turai.