in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CPI ya karu kana PPI ya ragu a Maris a Sin
2017-04-13 10:44:26 cri

Jiya Laraba hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar da alkaluma game da CPI wato yawan farashin kayayyakin da jama'a suke saya, da PPI wato yawan farashin kayayyakin masana'antun da aka samar, inda aka nuna cewa, a watan Maris na bana, adadin CPI ya karu da kaso 0.9 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, shi ma ya karu kadan idan aka kwatanta da watan Fabrairun bana, adadin PPI kuwa, duk da cewa, ya karu da kaso 7.6 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, amma ya ragu a cikin watanni uku da suka gabata. Masana da abin ya shafa suna ganin cewa, nan gaba CPI ba zai yi babban sauyawa ba a kasar Sin, PPI kuwa zai ci gaba da raguwa.

Bisa alkaluman da aka fitar jiya, an ce, adadin CPI wato yawan farashin kayayyakin da jama'a suke saya na kasar Sin ya karu da kaso 0.9 bisa 100 a watan Maris idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, amma ya ragu da kaso 0.3 bisa dari idan aka kwatanta da watan Fabrairun da ya gabata, masanan da abin ya shafa sun yi nuni da cewa, lamarin yana da nasaba da karuwar farashin kayayyaki da ba na abinci ba. A watan Maris, farashin kayayyaki da ba na abinci ba ya karu da kaso 2.3 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara a kasar Sin, a sa'i daya kuma, farashin abinci a kasar ta Sin ya ragu bisa babban mataki, har ya haifar da raguwar CPI wato yawan farashin kayayyakin da jama'a suke saya idan aka kwatanta da watan Fabrairun.

Shehun malamin cibiyar cudanyar tattalin arzikin kasashen duniya ta kasar Sin Wang Jun ya bayyana cewa, "Bayan bikin bazara na gargajiyar kasar Sin, farashin abinci ya ragu, hakan ya dace da yanayin da kasar ke ciki, ana iya cewa, farashin kayayyaki a watan Maris ko a cikin watanni uku na farkon shekarar bana bai yi babban sauyi ba."

Kamar yadda Wang Jun ya fada, adadin CPI wato yawan farashin kayayyakin da jama'a suke saya na watan Janairun bana na kasar Sin ya karu da kaso 2.5 bisa dari, a watan Fabrairu kuwa, ya karu da kaso 0.8 bisa dari, bai yi babban sauyi ba, yanzu dai an samu alkaluman na watanni 3 na farkon shekarar bana, wato adadin CPI wato yawan farashin kayayyakin da jama'a suke saya na kasar Sin a cikin wadannan watanni 3 ya karu da kaso 1.4 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara. Wang Jun yana ganin cewa, hakan ya nuna cewa, ba za a gamu da matsalar raguwar darajar kudi ba a wannan shekarar da muke ciki.

Game da PPI kuwa, a watan Maris, duk da cewa, adadin PPI wato yawan farashin kayayyakin masana'antun da ake samarwa ya karu da kaso 7.6 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, amma kason bai kai kason da aka samu a watan Fabrairun ba. Mataimakin babban jagoran aikin tattalin arziki na cibiyar cudanyar tattalin arzikin duniya ta kasar Sin Xu Hongcai yana ganin cewa, hakan ya nuna cewa, kila ne PPI zai fara raguwa. Xu Hongcai yana cewa, "Tun daga wannan wata, adadin PPI wato yawan farashin kayayyakin masana'antun da ake samarwa na kasar Sin ya fara raguwa, hakan ya dace da hasashen da aka yi, kamata ya yi zai ci gaba da raguwa a duk tsawon shekarar da muke ciki, bisa ga kiddidigar da aka yi, a watan Janairun bana, adadin ya karu da kaso 0.8 bisa dari idan aka kwatanta da watan da ya gabata, a watan Fabrairun bana, ya karu da kaso 0.6 bisa dari, a watan Maris kuwa, ya karu da kaso 0.3 bisa dari."

Ko da yake adadin PPI na watan Maris na kasar Sin bai karu bisa babban mataki ba, amma adadin CPI wato yawan farashin kayayyakin da jama'a suke saya ya karu, hakan ya sa dole ne mu fara gudanar da kwaskwarima kan tsarin farashin kayayyaki bisa manyan tsare-tsare a nan kasar Sin. Xu Hongcai yana mai cewa, "Hakan ya nuna cewa, adadin PPI wato yawan farashin kayayyakin masana'antun da ake samarwa na kasar Sin bai kawo tasiri ga dukkan fannonin masana'antu ba tukuna, misali, game da sha'anin hako danyen sinadari, farashinsu ya karu da kaso 33.7 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, a saboda haka wajibi ne a gudanar da kwaskwarima kan tsarin farashin kayayyaki, in ba haka ba, duk da cewa, farashin kwal ya karu, amma kamfanonin samar da lantarki ta hanyar yin amfani da kwal za su yi babbar hasara, kana kamata ya yi a gudanar da kwaskwarima kan tsarin farashin makamashi da albarkatun halittu, ta yadda za a kara kyautata tsarin tattalin arziki a kasar ta Sin."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China