in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Pakistan ta ce mutane 5 suka rasu sakamakon bude wutar da dakarun Indiya suka yi
2017-07-10 10:01:57 cri

Hukumomi a kasar Pakistan sun ce, adadin mutanen da dakarun kasar Indiya suka hallaka ya karu sakamakon mummunan bude wutar da dakarun suka yi a yankin LoC dake lardin Kashmir, adadin ya karu zuwa mutane 5.

Tun da farko rundunar sojin Pakistan da ma'aikatar harkokin wajen kasar sun tabbatar da mutuwar mutane a kalla biyu, wadanda aka kashe su a fada na baya bayan nan a yankin LoC a ranar Asabar.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ya sanar a ranar Lahadi cewa, an hallaka karin mutane 3, cikin su har da mata biyu, kuma an kashe mutanen ne a kauyukan Tetri Note da Chaffar, sannan an jikkata wani mutum guda.

Darakta janar mai kula da al'amurran kudancin Asiya a ma'aikatar harkokin wajen kasar Mohammad Faisal ya gayyaci mataimakin babban jakadan kasar Indiya J. P. Singh a ranar Lahadi, sannan ya kara yin Allah wadai da rashin amince da tsakaita bude wuta da dakarun Indiyan suka yi, lamarin da ya haddasa tashin hankali.

Kasashen Pakistan da Indiya sun amince da shirin tsakaita bude wuta ne a yankin LoC a shekarar 2003. Sai dai, dukkannin bangarorin biyu na zargin junansu da laifin kin mutunta yarjejeniyar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China