in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban magatakardar MDD ya kadu bisa gobarar tankar mai a Pakistan
2017-06-26 10:32:09 cri

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya nuna matukar damuwa, bisa tashewar da wata tankar mai ta yi a kasar Pakistan, lamarin da ya haifar da gobara da ta hallaka mutane a kalla 143, baya ga wasu 156 da suka jikkata.

Mr. Guterres wanda ya bayyana jimamin na sa ta cikin wata sanarwa da kakakin sa ya fitar a jiya Lahadi, ya kuma mika sakon ta'aziyyar sa ga iyalan wadanda lamarin ya shafa, da ma gwamnatin Pakistan, yana mai fatan samun sauki ciki sauri ga wadanda suka ji raunuka.

Ya ce, MDD na da burin tallafawa mahukuntan Pakistan ta dukkanin hanyoyin da suka dace domin shawo kan yanayin da kasar ta tsinci kan ta ciki.

Rahotanni dai sun tabbatar da cewa, hadarin gobarar tankar man ya auku ne a gundumar Bahawalpur dake lardin Punjab, da sanyin safiyar ranar Lahadi.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China