in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi Allah wadai da harin ta'addanci a makaranta dake Pakistan
2014-12-17 10:10:09 cri

Mahukuntan kasar Sin sun yi Allah wadai da harin da mayakan Taliban suka kai wata makaranta a yankin Peshawar dake kasar Pakistan, lamarin da ya haddasa rasuwar mutane kusan 141 da suka hada da dalibai 132.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, yana mai cewa, Sin na adawa da dukkanin wani aikin ta'addanci, za kuma ta ci gaba da goyon bayan Pakistan bisa duk wani yunkuri na yaki da 'yan ta'adda, da kare rayukan al'ummarta.

Shaidun gani da ido dai sun ce, mayakan Taliban din sanye da kakin soji sun yi wa makarantar dirar mikiya ne, inda nan take suka fara musayar wuta da masu gadi, kafin daga bisani su yi garkuwa da dalibai da ma'aikatan makarantar da dama. Lamarin da ya haddasa raunata a kalla mutane 245.

Tuni dai babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya bayyana takaicinsa game da aukuwar lamarin. Hakan kuwa na zuwa ne jin kadan bayan da kungiyar ta Taliban ta bayyana daukar alhakin kai harin. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China