in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Pakistan ta damkawa sojojin Najeriya jiragen sama masu horas da matuka 4
2016-12-06 10:08:24 cri

Hafsan hafsosin sojin saman kasar Pakistan Air Marshal Sohail Aman, ya mikawa rundunar sojin sama ta Najeriya wasu jiragen saman da ake amfani da su wajen horas da matuka 4.

Wata sanarwar da rundunar sojin Pakistan PAF ta fitar a jiya Litinin a Islamabad, babban birnin kasar ta bayyana cewa, dama kasashen Najeriya da Pakistan sun sanya hannu kan yarjejeniyar cinikin jiragen 10 a Abuja, babban birnin Najeriya a watan jiya.

Yarjejeniyar ta kunshi cinikin jiragen, da kuma ba da horo ga sojin saman Najeriyar. Kuma ana sa ran nan ba da jimawa ba PAF za ta kammala samar da jiragen baki daya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China